in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe na shirin farfado da zirga-zirgar jigaren sama tsakanin Harare da Beijing
2016-09-07 11:14:36 cri

Wani jami'in gwamnatin kasar Zimbabwe ya bayyana a kwanan baya cewa, kasar sa tana shirin farfado da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin birnin Harare, hedkwatarta zuwa birnin Beijing na kasar Sin, ta yadda masu yawon shakatawa da 'yan kasuwa Sinawa, za su samu saukin safara a kasar ta Zimbabwe.

Bisa labarin da aka bayar an ce, kamfanin jiragen saman Zimbabwe yana gudanar da shirin wannan aiki, kuma gwamnatin kasar ta yi imanin cewa, idan har an cimma nasarar farfado da wannan hanya ta sufuri, hakan zai baiwa masu yawon shakatawa da 'yan kasuwa karin dama ta ziyara da zuba jari a kasar.

Rahotanni na cewa, Zimbabwe ta gabatar da wata sabuwar manufa a watan Maris na bana, wadda ta ba da izini ga 'yan kasashe 36, ciki hadda kasar Sin, da su nemi Visa bayan sun sauka a kasar. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce yawan Sinawa da suka ziyarci kasar Zimbabwe a farkon rabin shekarar bana, ya karu da kashi 32 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China