Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya ce, darajar kudin Sin RMB ta dace da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
A cikin "rahoton shekarar 2016, dangane da barazanar da ake fuskanta a wajen kasa" wanda ausun ya kaddamar a jiya Laraba 27 ga wata, an yi nuni da cewa, a farkon rabin wannan shekara, darajar kudin RMB ta dan ragu, amma duk da haka a cewar IMF darajar RMB ta dace da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Kana kuma, rahoton ya yi hasashen cewa, sannu a hankali kasar Sin tana rage dogoro kan bukatun da ake da su a wajen kasar, yayin da bukatu suke kara karuwa a gida, don haka rarar kudin ciniki za ta ragu sannu a hankali a kasar ta Sin. Sa'an nan kuma sakamakon yawan al'ummar Sin dake fita kasashen ketare domin bude ido, ya sa gibin kudin cinikin ba da hidima zai kara karuwa a nan gaba. (Tasallah Yuan)