Taron G20 zai ci gaba da sa kaimi ga yin kwaskwarimar kason kasashe a IMF, in ji mataimakin shugaban babban bankin Sin
A yau Alhamis daya ga watan Satumba ne, mataimakin shugaban babban bankin kasar Sin, Yi Gang, ya bayyana cewa taron G20 dake tafe, zai ci gaba da sa kaimi ga yin kwaskwarima wajen inganta kason kasashe daban daban a asusun ba da lamuni na duniya (IMF), da tsarin gudanar da shi. Don haka a cewarsa, kamata ya yi a kyautata kason kasashe daban daban, don ya bayyana matsayin da kasashen duniya ke ciki ta fuskar tattalin arzikin duniya, tare da kara kason kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da na kasashe masu tasowa.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku