Asusun na IMF ya gabatar da sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya a wannan rana, inda ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya a bana zai kai kashi 3.1 cikin dari, yayin da a badi kuma zai kai kashi 3.4 cikin dari, wadanda suka yi kasa da adadin da aka yi hasashe a watan Afrilu na bana.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a sakamakon janyewar kasar Birtaniya daga kungiyar EU da sauran batutuwa, makomar kasashe masu ci gaban tattalin arziki ya shiga wani hali, amma an kiyaye bunkasuwar sabbin kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki da kasashe masu tasowa.
IMF ya yi hasashe cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 0.1 cikin dari zuwa kashi 6.6 cikin dari. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon gabatar da wasu matakan da za su taimaka wajen samar da ayyukan more rayuwa da bunkasuwar bada rancen kudi, wadanda za su taimaka wajen kyautata makomar bunkasuwar tattalin arziki na dan wani lokaci. Asusun na IMF yana ganin cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin a badi zai tsaya a kashi 6.2 cikin dari. (Zainab)