in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya bukaci kungiyar G20 da ta bullo da manufofin da za su bunkasa tattalin arzikin duniya
2016-07-22 11:36:05 cri

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20 da su bullo da manufofin da za su magance matsalolin da tattalin arzikin duniya ka iya fuskanta.

IMF ya kuma bayyana cewa, har yanzu ci gaban tattalin arzikin duniya yana tafiyar hawainiya, kuma shawarar da kasar Burtaniya ta yanke ta ficewa daga cikin kungiyar tarayyar Turai, ya kara nuna cewa, tattalin arzikin duniya yana iya fuskantar hadarin koma baya.

Wadannan bayanai na kunshe ne cikin rahoton nazari da asusun yake shirin gabatarwa taron ministocin kudi da gwamnonin manyan bankuna na kungiyar G20 da zai gudana a birnin Chengdu, babbar birnin lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin daga ranar 23 zuwa 24 ga wannan wata. Sai dai asusun na IMF ya canja hasashen da ya yi game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2016 da kuma 2017. Yanzu asusun ya yi kasa da hasashen nasa zuwa kaso 3.1 cikin 100 da kuma kaso 3.4 cikin 100. Ya ce ya yi hakan ne sakamakon rashin tabbas da ya dabaibaye batun ficewar kasar Burtaniya daga cikin kungiyar tarayyar Turai.

Bugu da kari, asusun na IMF ya yi gargadin cewa, za a fuskanci karancin samar da kayayyaki, jinkirin biyan basussuka, karancin zuba jari, karuwar rashin ayyukan yi, dalilan da asusun ya ce su ne suka haddasa koma bayan tattalin arzikin.

A saboda haka, IMF ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20 da su fito da managartan manufofin da za su farfado da ci gaba cikin dan karami da kuma dogon lokaci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China