Ya ce, a halin yanzu, babban kalubalen da Birtaniya, Turai da kasashen duniya suke fuskanta shi ne matsalolin da tattalin arziki da kasuwannin hada-hadar kudi ke fuskanta, sakamakon sauyin dangantakar dake tsakanin Birtaniya da kungiyar EU, bayan da kasar Birtaniya ta zabi ficewa daga kungiya ta EU. Haka kuma, babu tabbas kan irin illar da lamarin zai haifarwa kamfanonin kasashen duniya da abin ya shafa kafin kasar Birtaniya ta kulla sabuwar dangantaka a tsakaninta da kungiyar EU.
Haka kuma, Mr.Rice ya yi gargadi cewa, wadannan kalubalolin da ba a tabbatar da su ba a halin yanzu, za su haddasa raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, a saboda haka, ya bukaci kasar Birtaniya da kungiyar EU da su kawar da damuwar da gamayyar kasa da kasa ke nuna wa, kana su dukufa wajen kiyaye zaman lafiya a lokacin da aka samu sauyin dangantaka tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)