Shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMF Madam Christine Lagarde, ta yi kira ga kasashen duniya da su kara karfinsu a fannin yaki da cin hanci da karbar rashawa, don karawa jama'a kwarin gwiwa kan gwamnatocin su, da hukumomin kasuwanci, da sassa masu zaman kansu, da kafofin yada labarai, ta yadda za a sa kaimi ga raya duniya gaba bisa tsarin bai daya.
Madam Christine Lagarde ta bayyana hakan ne a jiya Lahadi, cikin jawabin da ta gabatar a gun taron lauyoyi na duniya, wanda ke gudana a shekara-shekara, inda ta bayyana cewa, tunanin gaza raya duniya bisa tsarin bai daya ya haifar da wata matsala mai tsanani, wato ta rashin amincewa game da hukumomin gwamnati, wanda shi ne babban dalilin da ya haifar da matsalar cin hanci da karbar rashawa a tsakanin hukumomin gwamnati da sassa masu zaman kansu.
Hakan ya sa, Christine Lagarde ta yi kira ga kasashe daban-daban da su kara karfinsu na gudanar da harkokin kudi cikin adalci, da yaki da halatta kudin haram, da kuma kara sa ido kan hukumomi masu kula da harkokin jama'a, da na 'yan kasuwa. A sa'i daya kuma, a sa kaimi ga ba da ilmi irin na ladabi da da'a, don dakile laifuka tsakanin hukumomin gwamnati, ko na sassa masu zaman kansu. (Amina)