in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
APC ta lashe zaben gwamnan jihar Edo
2016-09-30 10:06:04 cri

A jiya Alhamis ne hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta ayyana Godwin Obaseki na Jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Laraba.

Jami'in da ke bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kayode Soremekum ya ce, Godwin Obasaki ya lashe zaben ne da kuri'u 319,483, inda ya doke abokin takararsa na Jam'iyyar PDP Osagie Ize-Iyamu wanda ya samu kuri'u 253,173.

Mr. Soremukum ya ce, mutane 1,900,223 ne suka cancaci kada kuri'a, an kuma tantance mutane 662,039 a lokacin zaben, mutane 613,244 ne suka yi zabe, yayin da kuri'u 582,299 kuma suka lalace.

A jawabinsa, Obaseki ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta farfado da tattalin arzikin jihar, samar da ayyukan yi tare da inganta rayuwar jama'ar jihar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China