in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ya kara yawan tallafin da zai baiwa yara a arewacin Najeriya
2016-09-30 09:42:28 cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD(UNICEF) ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ya kara yawan kudaden agajin jin kai da zai samar a Najeriya, daga dala miliyan 55 zuwa dala miliyan 115.

Asusun ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne don ganin ya kai ga dukkan yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.

Asusun wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce yanzu an kara samun sabbin yankuna da ke jiran irin wadannan kayayyakin agaji sakamakon hare-haren Boko Haram, galibinsu kananan yara.

Darektan shirye-shiryen gaggawa na asusun UNICEF Afshan Khan, ya ce duk da matakan da suke dauka na samar da agajin jin kai, asusun yana bukatar taimako daga sauran kasashen duniya domin kara taimakon da ya bayarwa, musamman kananan yara da ke matukar bukatar taimako.

Rahotannin na nuna cewa, a wannan shekarar da muke ciki ta 2016, kimanin kananan yara 400,000 'yan kasa da shekaru biyar a jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya, za su fuskanci matsalar karancin abinci mai gina jiki. Akwai kuma sama da mutane miliyan hudu da ke fuskantar karancin abinci da kuma wasu mutane 65,000 da ke fama da yunwa, galibinsu a jihar Borno da rikicin Boko Haram din ya fi yiwa ta'adi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China