Najeriya na asarar dalar Amurka biliyan 200, sakamakon gaza zartas da dokar inganta harkokin da suka jibanci cinikayyar man fetur, kamar dai yadda wata cibiyar masana a fannin hakar ma'adanai ta bayyana cikin takardun binciken ta.
Bayanan sun kuma ja hankalin masu ruwa da tsaki game da lamarin, cewa Najeriyar za ta rika yin asarar da ta kai ta dalar Amurka Biliyan 15 a duk shekara, a fannin zuba jari saboda rashin tabbas ga dokokin da suka shafi cinikayyar man. (The Guardian)