in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu tsageru sun sake fasa wani bututun mai a kudu maso gabashin Najeriya
2016-09-29 20:25:37 cri
Wasu tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin mai a tarayyar Najeriya, sun ce su ne suka kaddamar da harin Bam kan wani bututun mai mallakar kasar, a jihar Delta dake kudu maso gabashin kasar.

Bututun man dai wanda aka lalata, na yankin Ughelli a jihar ta Delta, kuma kamfanin sarrafa albarkatun mai na kasar wanda ke karkashin kamfanin NNPC ne ke kula da shi.

Wata sanarwa da kungiyar tsagerun mai suna "Niger Delta Greenland Justice Mandate" ta fitar, ta ce ta aikata wannan danyen aiki ne domin nunawa duniya ikon da take da shi da yankin.

Kawo yanzu dai mahukuntan Najeriyar basu ce komai ba game da harin na baya bayan nan.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China