in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun damke masu yiwa Boko Haram leken asiri
2016-09-30 09:46:48 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar damke wani mutum da ke yiwa kungiyar Boko Haram leken asiri.

Da yake yiwa manema labarai karin haske game da kamen, mai magana da yawun rudunar sojan Najeriyar Kanar Sani Usman ya ce, ranar Laraba ce aka kama mutumin mai suna Majid Umar tare da wasu mutane uku a wata kasuwar kauye a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar. Mutanen sun kuma amsa laifin da ake tuhumarsu na kasancewa tare da kungiyar 'yan ta'addar.

Ana dai zargin mutanen ne da laifin taimakawa kungiyar wajen sayar musu da shanun da suka sata, daga bisani kuma su tura musu kudaden domin gudanar da ayyukansu na halaka jama'a.

Yankin arewa maso gabashin kasar dai ya kasance tungan kungiyar. Sai dai a 'yan watannin da suka gabata gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da hare-hare da dama da nufin kawar da 'ya'yan kungiyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China