in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taimaka wajen samar da tsaro a Afrika
2016-03-25 09:38:12 cri
A jiya Alhamis, kasar Sin ta mika gudumowar kayayyakin aikin soji, wanda aka kiyasta kudinsa dalar Amurka miliyan biyar, ga rundunar tabbatar da tsaro ta Afrika domin shirin tsaro na ko ta kwana a nahiyar.

Da yake jawabi a yayin bikin mika kayayyakin a Abuja, jakadan kasar Sin a Najeriya Gu Xiaojie, ya fada cewar, kasar Sin ta ba da gudumowar ne ga kungiyar raya ci gaban tattalain arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS, da nufin kara karfafa dankon dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen.

Jakadan na Sin ya fada cewar, a ko da yaushe kasar Sin a shirye take ta kulla kyakkyawar dangantaka tsakaninta da kasashen nahiyar Afrika, da sauran yankuna na shiyya-shiyya, domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar ta Afrika.

Mista Gu, ya fada cewar, wannan gudumowa da ma'aikatar tsaron kasar Sin ta bayar, ya nuna a fili irin dangantakar kut da kut dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da kungiyar ECOWAS, kuma wannan ya bayyana karara irin aniyar da Sin ke da ita wajen yin hadin gwiwa da ECOWAS domin samar da dawwaumamen zaman lafiya da tsaro a kasashen Afrika.

Bugu da kari, jakadan ya fada cewar, kasar Sin za ta ci gaba da tuntubar kasashen Afrika, da sauran kungiyoyi da hukumomi, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin nahiyar.

Gu ya ce gwamnatin Sin za ta ci gaba da samar da tallafi gwargwadon karfinta domin tallafawa kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China