in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saukaka kasuwanci da sufuri sun kasance wani jan aiki ga kasashen ECOWAS
2016-05-22 13:04:09 cri
Saukaka kasuwanci da sufuri na kasancewa a halin yanzu ga kasashen kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS) da hukumominta, wani babban kalubalen da ya kamata su tada, in ji mukadashin shugaba na farko na dakin kasuwanci da masana'antun Benin, Souley Yacoubou a ranar Asabar a Cotonou.

Samun sauye sauye cikin nasara da zamanintar da dokoki sun kasance wadanda ake jira domin saukaka kasuwanci da sufuri ta yadda za a kafa wani yanki mai kyau da takara, da aka kawar da duk wasu shingaye da samar da damammakin gaske ga kamfanoni, in ji mista Yacoubou.

Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a jajibirin dandalin shekara shekara karo na biyar na gamayyar Borderless 2016 kan taken "Dunkulewar shiyyar ta hanyar bunkasa kasuwanci da sufuri" mista Yacoubou ya bayyana cewa bunkasa tattalin arziki a yankin ECOWAS ya kasa fadada dalilin shingaye da dama.

Ya kuma nuna damuwarsa, kan lalacewar ababen more rayuwa, rashin nagartattun dokoki, rashin kwarewar ayyukan tashoshin ruwa, tsawon lokacin da kayayyaki suke dauka a tashar ruwa da kuma lokacin ratsa iyakoki, rashin tsaro da kuma yanayin bincike na 'yan sanda da kwastam. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China