Dandalin shugabannin matasan Afrika a Lome
Wasu daruruwan matasa da suka fito daga kasashe goma sha biyar na gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) na halarta a birnin Lome na kasar Togo, tun daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Satumban ga wani dandalin shugabannin matasa na yammacin Afrika (WALYS) karo na biyu, bisa taken "Matasa a teku: Wadannan irin hanyoyi domin fitar da Afrika daga matsala". Wannan haduwa, da kwararrun dake damuwa da ci gaban Afrika da kyautatuwar jin dadin matasa, suke jagoranta, na da manufar baiwa halartan samun bayanai, horo da nacewa kan hanyoyin da suka dace da karko kan tashin hankalin 'yan gudun hijira ba bisa doka ba dake tura nahiyar cikin zaman makoki. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku