Ofishin ECOWAS din ya bayyana wannan bukata ne yayin taron koli, na kungiyar da aka gudanar a birnin Dakar na kasar Senegal a ranar Asabar, kudurin ya yi nuni da cewa, halin tsaro da ake ciki a kasar Mali ya kara tsananta, wanda hakan ya haifar da damuwa ga kasashen duniya, tare da kawo barazana ga yanayin tsaro a daukacin yammacin Afirka.
Kudurin ya kara da cewa, kungiyar ECOWAS tana nazartar yiwuwar kafa sojojin hadin gwiwar kasa da kasa, don yaki da ta'addanci a kasar Mali tare. (Zainab)