Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana jiya Talata 27 ga wata cewa, muddin Najeriyar tana son fita daga matsalar tattalin arzikin da ta shiga, to, akwai bukatar kasar ta nemo rance, da rage kudaden da take kashewa, ta kuma kara fadada hanyoyinta na samun kudaden shiga.
Obasanjo wanda ya bayyana hakan a garin Abeokuta da ke yankin kudu maso yammacin kasar, ya ce, kudaden da kasar take kashewa sun zarta wadanda ke shiga lalitarta. Haka kuma ba ta tsimi saboda bacin rana.
Tsohon shugaban kasar ya kuma shawarci mahukuntan kasar, da su tuntubi kawayensu na ketare, don samun rance mai rangwame wanda zai taimaka wa kasar fita daga matsalar tattalin arzikin da ta fada a halin yanzu.
Ya kuma yi gargadin cewa, babu wata kasa da za ta yarda ta zuba kudadenta a kasar, muddin mahukuntan kasar ba su dauki matakai na zahiri game da yadda za su kawar da kalubalen da kasar take fuskanta ba. Bugu da kari, Obasanjo ya ce, wajibi ne Najeriyar ta koma ga aikin noma, maimakon dogaro ga man fetur domin kara samun kudaden shiga.
Tsohon shugaban kasar dai yana goyon bayan kiraye-kirayen da wasu ke yi na ganin an sayar da wasu daga kadarorin gwamnati domin samun karin kudade.(Ibrahim)