in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman Labarai daga wasu kafofin watsa labarun Najeriya
2016-09-26 19:06:30 cri
Ministar ma'aikatar kudin Najeriya Kemi Adeosun, ta ce ba za ta iya hasashen hakikanin lokacin da kasar za ta fita daga halin matsin tattalin arziki ba. (The Punch)

Rundunar sojojin Najeriya ta ce wata fashewa ta hallaka dakarun ta su 3, yayin da dakarun suka taka wasu nakiyoyi da aka binne, kana wasu mayakan Boko Haram suka auka musu a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar. (Daily Trust)

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya fidda wani sabon bidiyo, wanda a cikin sa yake karyata ikirarin da dakarun sojojin kasar suka yi a baya, na cewa sun lahanta shi. Bidiyon mai tsawon mintuna 38, wanda aka dora a kafar YouTube, ya nuna Shekau, tare da wasu mutane biyu rike da bindigogi, yana bayani kan manufofin kungiyar ta su. (Vanguard)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China