Mr. Enehikhuere wanda daya ne daga masana a cibiyar bunkasa ci gaba tsakanin Sin da Afirka, ya ce kasar Sin a matsayin ta na kasa ta biyu a fannin ci gaban tattalin arziki, tana da rawar takawa wajen agazawa Najeriya a wannan fanni.
Enehikhuere wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya kara da cewa kasancewar Sin babbar kawa ga Najeriya a fannin ci gaba, ana sa ran za ta taka rawar gani wajen magance matsalolin da Najeriyar ke fuskanta.
Ya ce kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya ta aminta da tsarin jagorancin Sin ta fuskar tattalin arziki, yayin da kuma kasar ke fatan koyi daga nasarorin da Sin din ta cimma a wannan fanni.(Saminu Alhassan)