in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labarun Najeriya
2016-09-27 19:04:16 cri
Kungiyar 'yan kwadago a Najeriya (NLC), ta ce zata jagoranci zanga zanga ta kasa baki daya, muddin gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cefanar da kadarorin kasar, kawai domin fidda kasar daga halin kamfar kudi da take fuskanta.

Shugaban kungiyar ta NLC Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan, yana mai cewa sayar da kadarorin kasar zai haifar da gagarumar matsala, muddin 'yan Najeriya basu dakatar da hakan ba. (The Punch)

Fannin hakar danyen mai a Najeriya ya gamu da sabon cikas a jiya Litinin, bayan da kamfanin Trans Niger ya dakatar da tura mai ta bututun sa wanda ke fidda danyen mai kimanin ganga 180,000 a ko wace rana, a matsayin wani matakin kandagarki, bayan da aka hangi tashin wata wuta a yankin Gio na al'ummar Ogoni. (Vanguard)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China