in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babban taro game da cinikin naman daji a Landan
2014-02-14 10:14:38 cri

Wakilai daga kasashe da yankuna fiye da 40 suka taru a birnin Landan na kasar Ingila domin halarta babban taro game da haramcin cinikin naman daji wanda zai amince da kawo karshen wannan mummunar sana'a.

Sakataren harkokin wajen Ingila William Haque wanda ya jagoranci taron ya bayyana cewa, haramcin ciniki na naman daji wani abun damuwa ne a duniya baki daya, kuma ya addabi kowa dake zaune a wannan zauren, don haka, a cewar shi, ya kamata dukkan mahalarta taron sun nuna wa duniya matukar amincewarsu a siyasance domin a shawo kan wannan mummunar sana'a kafin a makara.

A cikin wata sanarwar amincewa da aka fitar lokacin taron, an yi kira da a samar da wata hanya cikin gaggawa da za ta dakatar da safaran naman daji tare da murkushe duk wata kasuwa da aka fitar haramtacciya domin cinikin su ta hanyar hadin kan kasashe da kokarinsu na ganin hakan ya tabbata.

Manyan batutuwa a wajen taron sun samu amincewar wakilai daga kasashen Sin, Amurka, Rasha, Botswana, Chadi da Vietnam wadanda suka sha alwashin ganin sun taimaka da murkushe wannan sana'a ta hanyar hana bukatar amfani da sassan naman dajin a cikin abubuwan bukatunsu, inganta dokar da za ta hana hakan, sannan kuma za su taimaka da samar da rayuwa mai tsabta ga wadanda wannan sana'a ta fataucin naman daji ta shafa.

Wannan kudirin ya kuma hada da samar da karin goyon baya domin cigaban dokar kasa da kasa da ta haramta kasuwancin hauren giwa, hana gwamnati amfani da duk abin da ya kunshi namun dajin dake fuskantar barazanar karewa a doron kasa, sannan kuma da gyara dokokin da za su mai da fataucin namun daji da safarar su wani babban laifi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China