Achim Steiner ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta sha gabatar da dokokin kiyaye muhalli da dama, da tsara matakai don kare namun daji da tsirrai a nahiyar Afirka, don haka shugabannin kasashen Afirka suka yaba wa kasar Sin. Kana ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai ga kiyaye muhalli da samun bunkasuwa ba tare da gurbata yanayi ba, kuma wannan shi ne burin Sin da shirin kiyaye muhalli na MDD wato UNEP. (Zainab)