Wakilan kasashe 19, da na wasu hukumomin kasa da kasa sun halarci taron koli na kare giwayen nahiyar Afrika, wanda aka bude a jiya Litinin a birnin Kasane, wanda ke arewacin kasar Botswana, inda aka tattauna matuka game da ayyukan yaki da farauta ba bisa ka'ida ba, da hana cinikin hauren giwa, da kuma matakan kare giwayen nahiyar Afirka.
Wakilan kasashen Afirka da suka halarci taron sun nuna cewa, kasashen Afrika da dama, suna dukufa wajen daidaita matsalar zamantakewar dan Adam da giwaye, kana suna kokarin neman kyakkyawar hanyar raya tattalin arziki, domin cimma burin kara ba da gundummawa wajen kare giwayen.
Kaza lika, sun yi kira ga kasashe daban daban da su kara samar da goyon baya ga kasashen Afrika a fannonin zuba jari da bunkasa fasahohi.
A bangarensa, wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na kara daukar nauyin kare giwaye, ciki har da samar da kudaden taimako, da horar da ma'aikatan kare namun daji a Afrika, da kara yin musayar ra'ayi da hadin gwiwa tare da kasashen Afrika, domin gudanar da harkokin shari'a, da shawo kan matsalar fataucin sassan jikin namun daji a tsakanin kasashen duniya daban daban. (Lami)