in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya yi kira da a kauracewa bakin haure
2016-09-27 10:28:29 cri
Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya yi kira ga Misrawa da su tusa keyar duk wasu bakin haure da suka yi kokari shiga ko fita daga kasar Masar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake jawabi a bikin kammala aikin gine-gine a birnin Alexandria.

Al-Sisi ya bayyana haka bayan da wani kwale-kwale ya nutse a yankin tekun dake arewacin kasar Masar a kwanan baya, wanda ya haddasa rasuwar mutane kimanin dari biyu.

Bugu da kari, ya ce, abin da ya bata masa rai shi ne, wadannan matasa bakin haure sun shiga wannan mawuyacin hali tare da biyan kudade, a kokarin inganta rayuwarsu. A saboda haka, ya bukaci bangarori daban daban na kasar Masar da abin ya shafa da hukumomin kasar da su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, domin daidiata wannan matsala ta bakin haure.

A ran 21 ga wannan wata ne, wani kwale-kwale dauke da bakin haure ya nutse a yankin tekun bahar Rum na arewacin kasar Masar, wanda ya haddasa rasuwar mutane guda 178, kamar yadda jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta ruwaito.

Kaza lika, wani jami'in wurin ya bayyana cewa, a lokacin da hadarin ya auku, akwai mutane dari hudu zuwa dari shida a cikin wannan kwale-kwale, kuma, ana zaton kwale-kwalen yana kan hanyarsa ce ta zuwa kasar Italiya. Bayanai na cewa, kwale-kwalen ya nutse ne saboda adadin kaya da kuma mutanen da ke cikinsa sun zarce adadin da ya kamata ya dauka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China