Al-Sisi ya bayyana cewa, ya riga ya bada umurnin shugaba, inda ya bukaci gwamnatin kasar da ta hada kai da majalisar dokokin kasar wajen kammala yin bincike kan wannan daftarin doka, da bukatar hukumomin kiyaye tsaro na kasar da su dauki matakan yaki da masu fataucin mutane.
An yi hadarin nutsewar jirgin ruwa dake dauke da masu neman satar shigowa nahiyar Turai a tekun Atlantic na arewacin kasar Masar a ranar 21 ga wannan wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 164 ya zuwa ranar 24 ga wata.
Bayan hadarin, kasar Masar ta kama mutane 6 da aka zarge su da aikata laifin fataucin mutane da jigilar bakin haure. (Zainab)