Kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar Khaled Megahed ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, adadin yana iya karuwa,ganin cewa, har yanzu ana ci gaba da aikin ceto.
Bayanai na cewa, mahukuntan kasar Masar sun kama hudu daga cikin masu kwale-kwalen da ya kifen, bisa zargin su da laifin safarar mutane.
Hukumar kula da kan iyakokin kungiyar kasashen turai, ta yi gargadin cewa,yanzu haka ana kara samun bakin haure da ke kokarin shiga kasashen Turai ta tekun kasar Masar.
A ranar Larabar da ta gabata ce, wani kwale-kwale dauke da kimanin bakin haure 600 a kan hanyarta zuwa kasar Italiya ya kife a lardin Beheira da ke gabar tekun kasar Masar.(Ibrahim)