in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya yi taron bita da kwararrun Amurka
2016-09-21 13:39:37 cri

Da yammacin jiya Talata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gudanar da taron bita, tare da kwararru da masana na Amurka a fannonin tattalin arziki, da hada hadar kudi, da kafofin watsa labaru, inda suka yi musayar ra'ayi game da huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki, da cinikayya, da sauran al'amuran da ke jawo hankali.

Taron dai ya gudana ne a birnin New York na kasar Amurka. Kuma mutumin da ya kafa kamfanin Bloomberg, wato Mr. Michael Rubens, shi ne ya shugabanci taron.

A jawabin da ya gabatar, Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Amurka, kasa ce mai sukuni mafi girma a duniya, yayin da kasar Sin ke matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya. Don haka kiyaye, da raya kyakkyawar huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta fuskar siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, sun dace da babbar moriyar jama'ar sassan biyu. Haka kuma kasashen suna taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya, da bunkasuwa, da wadata a duk fadin duniya.

Firaministan kasar Sin ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin gudanar da gyare-gyare a gida, ciki hadda saukaka hanyoyin gudanarwa, da rarraba ikon gudanarwa zuwa matakai na kasa, da bada muhimmanci kan kiyaye ikon mallakar ilmi, da kara samar wa masana'antun ketare kyakkyawan yanayi na zuba jari a kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China