Ranar 19 ga wata da safe bisa agogon birnin New York na kasar Amurka, a hedkwatar MDD a birnin, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci taron manyan jami'a kan warware batun kwararar 'yan gudun hijira da baki daga wani wuri zuwa wani na daban, taron dai da ya kasance wani bangaren tarukan babban taron MDD karo na 71.
A yayin taron, mista Li ya ce, wannan shi ne taron manyan jami'ai karo na farko da MDD ta shirya tun bayan kafuwarta dangane da yadda za a tinkari batun kwararar 'yan gudun hijira da baki daga wani wuri zuwa wani na daban, wanda ya jawo hankalin kasa da kasa sosai. Batun 'yan gudun hijira da baki, wata matsala ce ta jin kai. Dole ne kasashen duniya su dauki matakan a-zo-a-gani wajen tallafawa 'yan gudun hijira. Ana bukatar kasashen duniya su inganta hadin gwiwa wajen warware batun 'yan gudun hijira da baki yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, wajibi ne a tabbatar da ganin hukumomin MDD sun taka rawarsu wajen taimakawa tsara da aiwatar da shirin daidaita batun daga dukkan fannoni, da kuma hada kai wajen yaki da shiga kasa ba bisa doka ba, fataucin jama'a, da ta'addanci. Ba za a iya warware batun 'yan gudun hijira da baki ba, sai idan kasashen da 'yan gudun hijira da baki suka fito sun tsaya wajen daukar matakai da kansu. Haka zalika wajibi ne sassa daban daban masu ruwa da tsaki su kawar da sabani ta hanyar yin tattaunawa, domin kawar da rikici ta hanyar yin shawarwari. Haka kuma, dole ne kasashen duniya su shiga tsakani a tsakaninsu, a kokarin taimakawa 'yan gudun hijira da kuma kasashen da suka fito domin samun dawamammen zaman lafiya da mulki nagari. A cewar mista Li, kamata ya yi kasashen duniya su bude kofarsu ga waje, su raya kasa tare da samun nasara tare, su rage rashin daidaito a tsakanin kasa da kasa ta fuskar bunkasuwa, a kokarin kara azama kan samun ci gaba tare.
Firaministan na kasar Sin ya kuma jaddada cewa, har kullum kasarsa ta Sin tana sa muhimmanci sosai da kuma shiga ayyukan warware batun 'yan gudun hijira da baki cikin himma. Kasar Sin za ta dauki jerin matakan jin kai, da yin tattaunawa kan hadin gwiwa da hukumomin kasa da kasa da kasashe masu tasowa da batun ya shafa a fannin warware batun yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)