Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin New York na kasar Amurka a ranar Lahadi domin halartar babban taron MDD karo na 71.
A yayin rangadin nasa a New York, Li Keqiang zai gabatar da matsayin kasar kan manyan batutuwan dake da nasaba da tsarin duniya, shugabancin duniya, zaman lafiya da ci gaba, a cikin jawabinsa a yayin babbar mahawara karo na 71 na babban taron MDD.
A yayin wannan taron kuma, firaministan kasar Sin zai sanar da muhimman matakan kasar Sin domin tallafawa kokarin MDD da kuma fuskantar kalubalolin duniya.
Halartar Firaministan kasar Sin a babban taron MDD na kasancewa daya daga cikin muhimman tarukan diflomasiyya na kasar a cikin wannan shekara a fagen kasa da kasa, kuma ta shaida muhimmacin da kasar Sin take nunawa ga MDD da kuma harkokin kasa da kasa, in ji mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong a ranar Laraba.
Wannan shekara ita ce ta cikon shekaru 45 da maido da kujerar kasar Sin a MDD. (Maman Ada)