in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya jagoranci taron tattauna kan samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030
2016-09-21 08:59:57 cri

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya jagoranci taron samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 a yammacin ran 19 ga wata a birnin New York, hedkwatar MDD. Babban magatakardan majalisar Mista Ban Ki-Moon, shugaban babban taron majalisa karo na 71 Peter Thomsen da dai sauran jami'an da suka fito daga muhimman hukumomin majalisar da muhimman kungiyoyin kasa da kasa sun halarci taron.

Yayin taron, Mista Li ya bayyana cewa, ya kamata an mai da aikin kawar da talauci da yunwa da dai raguwar wasu ayyuka a matsayin wani muhimmin aiki a gaban kome, da sa kaimi ga a samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata, da samun daidaito tsakanin tattalin arziki, al'umma, muhalli bisa tsari mai yakini, ta yadda za a fidda wata hanya mai kyau wajen samun bunkasuwar tattalin arziki mai wadata da al'umma mai ci gaba da kuma muhalli mai kyau.

Ban da wannan kuma, Mista Li ya jaddada cewa, ya kamata a nace ga hadin gwiwa tsakanin kasashe masu wadata da masu tasowa, wanda ya zama wani muhimmin mataki, a bangare daya kasashe masu wadata ya kamata su cika alkwarinsu na goyon bayan kasashe masu tasowa da su zabi hanyar da ta fi dacewa halayyarsu don samun bunkasuwa. A wani bangare na daban kuwa, kasashe masu tasowa kuma, ya kamata su  zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu don cimma burinsu na dogaro da kansu cikin hadin gwiwa.

Mista Li ya kara da cewa, a cikin shekaru goma sha biyar da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta mai da muhimmanci sosai da kuma kasancewa abin koyi ga sauran kasashe domin cimma muradun karni na MDD, kuma ta samu ci gaba mai yakini wajen rage talauci, kiwon lafiya, ba da ilmi da dai sauransu. Matakin da ya sa mutane fiye da miliyan 400 sun fita daga kangin talauci, yawan yara da suka mutu masu kasa da shekaru biyar sun ragu da kashi 2 cikin 3, yayin da yawan mata masu juna biyu da suka mutu ya ragu da kashi 3 cikin 4, ban da wannan kuma, Sin ta kafa wani tsarin kula da tsofaffi da ba da tabbaci kan aikin jinya, wanda ya fi girma a duniya. Dadin dadawa Sin ta riga ta fara gudanar da ayyuka wajen tabbatar da ajandar samun dauwamammen bunkasuwa kafin shekarar 2030 a dukkan fannoni, kana kuma ta amince da shirin tabbatar da samun dauwamammen bunkasuwa kafin shekarar 2030 bisa halin da kasar Sin ke ciki, nan gaba kuma za a kaddamar da shirin, matakin da ya baiwa Sin jagoranci wajen gudanar da ayyukan kan tabbatar da shirin. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China