in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta daina kokarinta ba domin sa kaimi ga cigaba da zaman lafiya a duniya
2016-09-19 11:16:41 cri

Daga ranar 18 zuwa 21 ga watan Satumba, Firaministan kasar Sin Li Keqiang zai halarci babbar muhawarar shekara-shekara karo na 71 ta babban taron MDD, kuma zai gabatar da matakan da kasar ta dauka dake shafar bunkasa zaman lafiya da cigaban gamayyar kasa da kasa, in ji wani jami'in diflomasiyyar kasar Sin a ranar Lahadi a birnin New York.

Liu Jieyi, wakilin dindindin na kasar Sin da ke zaune a MDD, ya bayyana a yayin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, a matsayin wata kungiyar kasa da kasa, mafi karfin wakiltar duniya, MDD ta taimaka sosai wajen kiyaye zaman lafiya a duniya da kuma bunkasa cigaban hadin gwiwa tun bayan kafuwarta a shekarar 1945.

Wannan shekara na kuma kasancewa ta cikon shekaru 45 da maido da kujerar kasar Sin a MDD. A matsayin wata kasa mai goyon baya da kuma nacewa ga harkokin kasa da kasa, kasar Sin za ta ba da taimako matuka wajen kiyaye zaman lafiya a duniya da kuma bunkasa cigaba, in ji jami'in diflomasiyyar kasar Sin.

Na farko, Sin za ta jagoranci cigaba da dangantakar kasa da kasa, kuma za ta himmatu wajen aiwatar da ajandar cigaba mai karko na shekarar 2030. Na biyu, Sin na shirin taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Na uku kuma, Sin na goyon baya sosai ga MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China