Ranar 19 ga wata da yamma bisa agogon birnin New York na kasar Amurka, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Amurka Barack Obama, inda suka yi musayar ra'ayoyi dangane da dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 da kuma al'amuran kasa da kasa da yankuna wadanda suka jawo hankalinsu sosai.
A yayin ganawarsu, mista Li ya yi nuni da cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya ta dasa harsashi mai kyau wajen raya huldar da ke tsakaninsu, yayin take kara azama kan bunkasa huldarsu. Don haka wajibi ne kasashen 2 su sa kaimi kan kawo karshen shawarwarinsu dangane da yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da Amurka tun da wuri. Sa'an nan dole ne kasashen 2 su daidaita sabani ta fuskar tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata.
Haka zalika, firaministan kasar Sin ya sake nanata ka'idar da kasar Sin take bi game da batutuwan yankin Taiwan da jihar Tibet, tare da fatan cewa, Amurka za ta tinkari batutuwan yadda ya kamata.
A nasa bangaren kuma, shugaba Obama ya ce, kasashen Amurka da Sin suna raya huldar da ke tsakaninsu ba tare da tangarda ba, lamarin da ya nuna muhimmanci sosai gare su da ma duk duniya baki daya. Huldar da ke tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki tana taimakawa raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 cikin zaman lafiya. Kasarsa ta Amurka tana mara wa kasar Sin baya wajen yin gyare-gyare a cikin gida.
Har ila yau shugaban na kasar Amurka ya sake nanata cewa, gwamnatin Amurka tana bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya", kuma ba za ta canza manufarta ba.
Ban da haka kuma, bangarorin 2 sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan samun ci gaba mai dorewa, 'yan gudun hijira, kiyaye zaman lafiya da dai sauransu. (Tasallah Yuan)