in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai halarci babban taron MDD tare da kai ziyara kasashen Canada da Cuba
2016-09-18 14:23:06 cri
A yammacin yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya tashi zuwa birnin New York na kasar Amurka don halartar babban taron MDD karo na 71, kana daga bisani zai kai ziyarar aiki zuwa kasashen Canada da Cuba.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar ta nuna cewa, firaminista Li zai gudanar da rangadin ne daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Satumba, bisa gayyatar babban sakataren MDD da takwaransa na kasar Canada Justin Trudeau da kuma shugaban kasar Cuba, kana jagoran majalisar ministocin kasar Raul Castro bi da bi.

Firaminista Li dai zai gudanar da wannan rangadi ne tare da rakiyar mai dakinsa Cheng Hong. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China