Wata sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labarai a birnin Legas cibiyar kasuwancin kasar, ta ce tana fatan ikararin gwamnatin tarayyar Najeriya na sasantawa da mayakan Boko Haram zai kai ga tabbatar da fatan sake ganawar 'yan matan da iyayensu.
Sakataren kungiyar Muhammad Askira, ya yaba da rawar da sojojin Najeriya suka taka na kawar da 'yan ta'addan Boko Haram daga maboyarsu, da ma matakan shugaba Muhammadu Buhari na yaki da masu tayar da kayar baya a kasar.
Askir ya ce, suna fatan nan ba da dadewa ba 'yan matan na Chibok da ke hannun mayakan Boko Haram za su sake haduwa da iyayensu.(Ibrahim)