in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin Boko Haram ya yi tasiri kan dubban yaran dake yankunan tafkin Chadi
2016-08-26 09:33:05 cri

Asusun yara na MDD UNICEF, ya yi kashedin cewa hare haren da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a baya, sun yi mummunan tasiri ga rayuwar yara kanana dake zaune a yankunan tafkin Chadi.

Wannan kashedi dai na kunshe ne cikin wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar, wanda kuma ya nuna cewa yanayin matsi da al'ummar yankin suka fuskanta a baya, ya tilasawa kimanin mutane miliyan 1 da dubu dari 4 barin gidajen su, kana wasu miliyan guda ke makale a yankuna masu wuyar shiga.

Kaza lika rahoton ya nuna cewa a wannan shekara ta bana, akwai yara kanana da yawan su ya kai rabin miliyan, wanda ke fama da kamfar abinci mai gina jiki, adadin da ya haura mutum 175,000 da aka samu a farkon shekarar.

A daya hannun kuma a dai shekara ta bana, rahoton na UNICEF ya nuna cewa an yi amfani da yara kanana kimanin 38, domin aiwatar da hare haren kunar bakin wake a yankin.

Game da kudaden da asusun ke bukata wajen gudanar da shirye shiryen sa kuwa, UNICEF ya ce irin wadannan kudade sun yi karanci matuka, duba da yadda a yanzu ake samun karin yankuna dake neman agaji, sakamakon fatattakar mayakan Boko Haram daga yankuna masu yawa, da dakarun hadin gwiwar yankin ke yi musamman a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai asusun ya karbi kaso 13 bisa dari ne kacal, daga jimillar kudin da yawan sa ya kai dalar Amurka miliyan 308, wadanda ake bukata domin tallafawa al'ummun da rikicin Boko Haram ya shafa a kasashen Najeriya, da Nijar, da Chadi da kuma Kamaru. Wannan rahoto dai na zuwa ne gabanin taron MDD game da batun 'yan gudun hijira, wanda za a yi a ranar 19 ga watan Satumbar dake tafe.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China