in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta lalata wata maboyar 'yan ta'addan Boko Haram
2016-09-03 14:11:22 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana a ranar Jumma'a cewa ta lalata wani sansanin 'yan Boko Haram dake jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar cikin nasara, a yayin da sojojin kasar suka kai wani harin ba tsammani kan maboyar 'yan ta'addan.

Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF), Ayodele Famuyiwa, ya nuna a cikin wata sanarwa, inda bayanai suka nuna cewa kamandojin Boko Haram da suke jikkata a cikin wani harin ranar 20 ga watan Augustan da ya gabata, da alamun cewa suna karbar jinya a wannan sansani.

Mista Famuyiwa ya nanata cewa samamen bayan nan nada manufar dakile shugabannin kungiyar.

A cewarsa, har yanzu sojojin saman basu tantance yawan mutunen da harin ya shafa ba, amma tagawar kimanta barnar da ta biyo bayan wannan samame ta kasance mai tsanani sosai domin gine gine sun kone kamar yadda wani bidiyon da aka fitar ya nuna na wannan harin da aka kai ta sama.

Dakarun Najeriya sun gudanar da sintirin sanya ido ta sama da kuma ta kasa a jihar Borno da kuma dukkan yankin arewa maso gabashi, hedkwatar Boko Haram tun a shekarar 2009. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China