in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zargi Boko Haram da kashe mutane 5 a jamhuriyar Nijer
2016-09-04 12:51:29 cri
Mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu a daren Jumma'ar da ta gabata a wani harin da ake zargin kungiyar Boko Haram da kaddamarwa a gabashin jamhuriyar Nijer.

Gidan radiyon gwamnatin jamhuriyar ta Naijer ya rawaito cewa, an yi amana maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne, inda suka afkawa kauyen Toumour yayin da suke haye kan rakuma a daren Jumma'ar da ta gabata. Maharan, sun kona gidaje masu yawa, sannan sun kashe jama'a da kuma jikkata wasu da dama daga cikin mazauna kauyen.

Gidan radiyon kasar ya sanar da cewa, wannan shi ne karon farko da kungiyar ta kaddamar da hari a gabashin jamhuriyar Nijer cikin watanni uku. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China