Kafin bude taron mahawara a tsakanin kowa, an kalli wani bidiyo a babban dakin taron MDD, domin tunawa da cikar shekara daya da zartas da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030.
Haka kuma, a yayin da yake ba da jawabi, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a halin yanzu, gamayyar kasa da kasa suna dukufa wajen cimma burin neman dauwamammen ci gaba, har akwai gwamnatoci na kasashe fiye da guda 50 da su shigar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 cikin ayyukansu, shi ya sa, ya bukaci kasa da kasa da su gaggauta zartas da yarjejeniyar Paris ta fuskar sauyin yanayi, ta yadda yarjejeniyar za ta fara aiki kafin karshen shekarar bana.
Haka zalika, Ban Ki-moon ya ce, rikicin kasar Syria ya riga ya haddasa rasuwa da jikkatar mutane masu yawa, yayin da kuma ya haifar da tashe-tashen hankula a yankin, amma ba za a iya warware rikicin ta hanyar soja ba, shi ya sa, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su kawo karshen ricikin dake tsakaninsu, sa'an nan, su fara yin shawarwarin neman sulhu da sauri.
Bugu da kari, shugaban babban taron MDD karo na 71 Peter Thomsen ya ce, ya kamata a gaggata aiwatar da shirinmu na neman dauwamammen ci gaba, ya kuma yi kira da a gaggauta wannan aiki ta hanyoyin samar da ilmi ga matasa, kara yin amfani da kayayyakin more rayuwa, karfafa ayyukan tsara shirye-shirye, sabunta fasahohin da abin ya shafa, wanzar da zaman lafiya mai dorewa da dai sauransu. (Maryam)