in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya sabunta wa'adin aikin tawagar UNMIL
2016-09-15 12:28:52 cri
Kwamitin tsaron MDD ya tabbatar da sabunta wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, wadda ke aiki a kasar Liberia zuwa karshen wannan shekara ta 2016. Hakan dai ya biyo bayyana amincewar da kudurin ya samu daga mambobin sa 15, wadanda suka hakikance da barin yawan dakarun tawagar ta UNMIL a yadda suke a yanzu, wato 'yan sanda da sojoji 1240, tare da sauran jami'ai 606.

Kwamitin na tsaro dai ya bayyana cewa bayan sabon wa'adin, za a janye dakarun tawagar ta UNMIL, a kuma maye gurbinsu da wani shiri na MDD, bayan nazarin halin da ake ciki, aikin da ake fatan aiwatarwa a tsakiyar watan Nuwambar dake tafe.

Tuni dai kwamitin na tsaro ya mika bukatar gudanar da bincike, game da yanayin da kasar ta Liberia ke ciki ga babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, da ma bukatar sake yin duba na tsanaki kan tsarin da za a bi na maye gurbin tawagar dake aikin wanzar da zaman lafiya yanzu haka a kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China