in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli kan batun 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani na MDD ya zartas da sanarwar siyasa
2016-09-20 10:59:03 cri
Taron kolin dake kula da harkokin kaurar 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani na babban taron MDD ya zartas da wata sanarwar siyasa a jiya Litinin 19 ga wata, inda gamayyar kasa da kasa suka yi alkawarin cewa, za su karfafa ayyukansu wajen warware matsalar 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani, kana za su tsara shirin tinkarar matsalar 'yan gudun hijira daga dukkan fannoni.

A wannan rana kuma, taron kolin ya zartas da sanarwar New York ta batun 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani ta hanyar kudurin babban taron MDD, sa'an nan, gamayyar kasa da kasa su yi alkawura da dama da abin ya shafa, cikin har da kiyaye 'yancin 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani, samar da taimako ga kasashen dake karbar wadannan baki, jaddada gudummawar da baki suke bayar, yayin da ake kyautata ayyukan ba da taimakon jin kai da dai sauransu.

Kana, bisa wannan sanarwar din, an ce, gamayyar kasa da kasa za su fara wani yunkurin yin shawarwari a tsaknin gwamnatocin kasa da kasa, inda ake sa ran kulla wata yarjejeniyar kan harkokin kaurar jama'a ta kasa da kasa a shekarar 2018, wadda za a iya aiwatar da ita cikin zaman lafiya, kuma yadda ya kamata.

Haka zalika, a yayin taron kolin din da aka yi, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon da shugaban kungiyar dake kula da harkokin kaura ta kasa da kasa William Lacy Swing sun kulla yarjejeniyar dangantakar tsakanin MDD da kungiyar harkokin kaura ta kasa da kasa a hukunce, lamarin da ya nuna cewa, kungiyar ta shiga MDD a hukunce tun daga wannan rana.

Taron kolin da aka yi a ranar 19 shi ne taro mafi girma da aka taba yi cikin MDD dangane da batun 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani, wanda shugaban babban taron MDD na wannan karo Peter Thomsen da kuma tsohon shugaban babban taron MDD Mogens Lykketoft suka ba da jagorancin taron cikin hadin gwiwa, haka kuma, manyan jami'an bankin duniya, kungiyar dake kula da harkokin kaura ta kasa da kasa, da kuma jami'an dake kula da harkokin 'yan gudun hijira, hakkin dan Adam, da mata na MDD da kuma wasu wakilan 'yan gudun hijira sun halarci bikin bude taron. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China