Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ce ta bayyana hakan a nan birnin Beijing, Ta kuma bayyana cewa, Mr Li zai fara rangadin nasa ne daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Satumba.
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon,Firaministan kasar Canada Justin Trudeau da shugaban kasar Cuba kana jagoran majalisar ministocin kasar Raul Castro Ruz ne suka gayyaci firaminista Li Keqiang bi da bi.(Ibrahim)