Da yake karin haske game da hakan, mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Li Baodong, ya ce cikin jawabin da zai gabatar a yayin taron muhawara a MDD, Mr. Li Keqiang zai fayyace manufofin kasar Sin game da harkokin da suka jibanci jagorancin duniya, da dokokin kasa da kasa, da ma irin matakan da kasar ta Sin ke dauka wajen tunkarar kalubalolin da duniya ke fuskanta.
Mr. Li Baodong ya kara da cewa firaministan na Sin zai zanta da wasu jagororin kasashen duniya a birnin New York. Ya ce Sin na fatan amfani da wannan dama wajen karfafa alakarta da sauran sassa na duniya, tare da kara fahimtar juna game da manufofi na diflomasiyyar kasa da kasa.
Jami'in ya ce ta haka ne kasashen duniya za su kara fadada hadin gwiwar su a fannin jagorancin duniya yadda ya kamata. (Saminu Hassan)