Hukumar kididdiga ta kungiyar tarayyar kasashen Turai ta fidda wani rahoto a ran 2 ga watan, dake cewa, a shekarar 2015, akwai yara 'yan gudun hijira wadanda ba su samu rakiyar iyalansu ba, sama da dubu 90 da suke neman takardar mafaka daga mambobin kasashen kungiyar EU guda 28 da kuma kasashen Schengen guda 4 da suka hada da Iceland, Liechtenstein, Norway da Switzerland.
Kididdiga na nuna cewa daga shekarar 2008 zuwa 2013 wannan adadi ya kai dubu 10, amma ya zuwa shekarar 2014, adadin ya ninka har sau biyu.
Kaza lika, kashi 91 bisa dari daga cikin wadannan yara 'yan gudun hijira maza ne, sannan galibinsu 'yan gudun hijira ne daga kasashen Afghanistan da Syria, kuma adadin zai kai sama da dubu 45 da kuma dubu 14. Haka kuma, adadin 'yan gudun hijirar da su kan nemi iznin shiga kasar Switzerland, ya kai kimanin dubu 35, wanda ya kai kashi 40 bisa dari cikin takardun iznin da 'yan gudun hijira suka gabatar, sai kuma, kasashen Jamus, Hungary, Austria, Norway da kuma Italy da ke biye.
Bugu da kari, kafofin watsa labarai na kasar Faransa sun bayyana cewa, a shekarar 2015 yara 'yan gudun hijira kimanin 320 sun gabatar mata da takardun bukatar neman izinin shiga kasar, lamarin da ya sa kasar ta kasance ta 15 cikin kasashe guda 32 wadanda suke karbar 'yan gudun hijira a halin yanzu. (Maryam)