A cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, yanzu mutane sama da miliyan 65 a duniya sun yi gudun hijira domin kauracewa rikice-rikice da nuna karfin tuwo da sauransu, har ma sun nemi tsirar da rayukansu ta hanyar ratsa iyakar kasa. Wasu sun yi gudun hijira cikin dogon lokaci, sabo da rashin daidaita rikice-rikice da ake fuskanta.
A nasa bangare, Mr. Lykketoft ya furta a jawabinsa cewa, rikici ya zama babban dalilin dake haifar da bukatun jin kai, dole ne kasashen duniya su kara kokarin daidaita rikici ta hanyar siyasa. Ya yi kira ga kasashen duniya da su kara nuna goyon baya ga MDD da sauransu, domin tinkarar manyan bukatun jin kai, tare da jaddada muhimmanci na bayar da tarbiya ga yara masu gudun hijira, da taimakawa kasashen da ke karbar 'yan gudun hijira, da daina nuna bambanci domin kara samun hakuri.
A wannan rana, an kaddamar da bikin nune nune dangane da rayuwar 'yan gudun hijira a duniya a babban dakin masu yawon shakatawa na MDD. (Fatima)