Hukumar ta UNHCR ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na shekara-shekara, wanda ya bibiyi mutanen da aka tilastawa barin muhallansu a fadin duniya,inda kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara ke kan gaba wajen yawan mutanen da suka bar nasu muhallan a shekarar 2015, wadda ke biye da yankin gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afirka.
Hukumar ta ce kazamin fadan da ya barke a kasar Sudan ta Kudu a shekarar 2015 da Jamhuriyar Afirka ta taskiya da kuma kasar Somaliya, baya ga wasu tarin mutanen da suka bar muhallansu a kasashen Najereiya da Burundi da Sudan da Jamhuriyar demokiradiyar Congo da Mozamboique baki daya ya kai mutane miliyan 18.4 na wadanda ke gudun hijira da wadanda aka tilastawa barin matsugunasu ya zuwa karshen wannan shekara.
A yau Litinin ne hukumar ta fitar da wannan rahoto a birnin Nairobi na kasar Kenya a daidai lokacin da duniya ta ke bikin ranar 'yan gudun hijira ta duniya, inda ta bayyana cewa, a halin yanzu akwai 'yan gudun hijira kimanin miliyan 4.4 da ke samun mafaka a kusan dukkan kasashen Afirka da ke kudu da hamadar sahara fiye da sauran yankuna na duniya.
Daga karshe ya kuma bayyana cewa, a duk fadin duniya, kimanin mutane miliyan 65.3 ne suka bar muhallansu a shekara 2015, idan aka kwatanta da mutane miliyan 59.5 kadai da suka rasa muhallansu a shekarar 2014.(Ibrahim)