in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kwashe 'yan gudun hijiran Somaliya fiye da dubu 24 daga Kenya
2016-08-25 10:27:03 cri

Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta sanar da cewa, 'yan gudun hijiran Somaliya fiye da dubu 24 ne aka kashe daga kasar Kenya tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar bangarori uku.

Da yake magana a ranar Laraba a cikin sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab dake arewa maso gabashin Kenya, mataimakin wakilin ofishin HCR dake Kenya, Wella Kouyou, ya nuna cewa, kimanin 'yan gudun hijiran Somaliya dubu 18 suka koma kasarsu a wannan shekara tun lokacin HCR ta gaggauta kamfen kwashe 'yan gudun hijira dake bukata.

HCR za ta yi aiki tare da gwamnatocin Kenya da Somaliya domin ganin cewa, komawar 'yan gudun hijira ta gudana bisa son rai kuma cikin girmama 'yancin dan adam.

Dadaab, ya kasance sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya, an kafa shi a Kenya yau da fiye da shekaru ishirin da suka gabata domin karbar mutanen dake tserewa rikicin Somaliya.

Gwamnatin Kenya ta sanar a wannan shekara cewa, za ta rufe wannan sansani, tare da kwashe daukacin 'yan gudun hijiran Somaliya dake rayuwa a wurin, da yawansu ya kai fiye da dubu 300, bisa dalilai na tsaro da kare muhalli.

Kenya ta bayyana cewa, mambobin kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya sun shiga cikin sansanin Dadaab, kuma suna amfani da wurin a matsayin sansaninsu. Kungiyar Al-Shabaab ta kai wani kazamin hari kan jami'ar Garissa, dake arewa maso gabashin Kenya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148 a cikin watan Afrilun da ya gabata, yawancinsu dalibai ne.

HCR, Kenya da Somaliya sun rattaba hannu a shekarar 2014 kan wata yarjejeniyar kwashe 'yan gudun hijiran Somaliya bisa son rai, amma shirin yake tafiyar hawainiya har zuwa wannan lokaci.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta zai jagoranci wata tawagar Kenya domin shiga babban taron MDD a cikin wata mai zuwa, inda za a tattauna matakan kwashe 'yan gudun hijira, da zummar ganin zai samu goyon baya kan wannan batu, in ji ministan cikin gidan Kenya, Joseph Nkaissery. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China