Mr. Jurgenson ya bayyana haka ne, a yayin taron kolin jin kai na kasa da kasa karo na farko da aka bude a birnin Istanbul na kasar Turkiya a wannan rana. Haka kuma, a yayin taron kolin, an kira wani taro mai taken "kare ko wane yaro da ko wace yarinya, neman ci gaba yayin da ake kiyaye yanayin jin kai yadda ya kamata".
Bugu da kari, babbar sakatariyar hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al'ada ta MDD wato UNESCO Irina Bokova, ta yi fatan cewa, gamayyar kasa da kasa za su iya kara yawan taimakon kudi da suke baiwa MDD, domin kyautata ayyukan koyar da yara.
Kaza lika, bisa kididdigar da aka yi, an ce, a halin yanzu, adadin yaran da ba sa iya zuwa makarantu a duniya ya kai miliyan 123, kuma yara kimanin miliyan 168 suna aikin karfi domin karancin kudi. Har wa yau adadin yaran da ake sayar da su ya kai kimanin miliyan 1.2 a ko wace shekara. (Maryam)