in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR: nutsewar wani jirgin ruwa a tekun Bahar Rum zai iya haddasa mutuwar mutane a kalla 500
2016-04-21 11:26:10 cri
Hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta ba da rahoto a jiya Laraba cewa, wani jirgin ruwa na kasar Libya dake satar shiga kasar Italiya ya nutse a makon da ya gabata, watakila wannan hadari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 500.

Rahoton ya ce, jami'an hukumar UNHCR sun gana da mutane 41 da suka tsira da rayukansu daga wannan hadari a shekaran jiya, wadanda suka bayyana cewa, sun dauki wani karamin jirgin ruwa a lokacin farko, daga bisani, an nemi su shiga wani babban jirgin ruwa dake dauke da mutane fiye kima, jirgin ruwa ya nutse ne a lokacin da aka shiga cikinsa.

Daga cikin wadannan mutanen da suke tsira, wasu ba su shiga babban jirgin ruwa ba, wasu daga cikinsu sun tsalle daga babban jirgin ruwa har sun yi iyo zuwa karamin jirgin ruwan. Sun taso kan ruwa har kwanaki 3, wani jirgin ruwa na kasuwanci ya cece su a ranar 16 ga wata.

Hukumar UNHCR ta bayyana cewa, wadannan mutane 41 sun fito ne daga kasashen Somaliya da Habasha da Masar da kuma Sudan, a halin yanzu, an tsugunar da su a wani dakin motsa jiki na wani tsibirin kasar Greece.

Bisa kididdigar da kungiyar makaurata ta duniya ta bayar, an ce, mutane 732 sun mutu a lokacin da suke satar shigo nahiyar Turai a wannan shekara a tekun Bahar Rum.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China