in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya binciki yadda ake fama da bala'in fari da ambaliyar ruwa
2016-07-31 12:00:18 cri
A ranar Jumma'a 29 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi rangadin aiki zuwa helkwatar hukumar kula da bala'in fari da ambaliyar ruwa ta kasar Sin da ke nan Beijing, inda ya binciki yadda ake fama da bala'in ambaliyar ruwa, kuma ya ba da umurnin tsara sabon shirin cigaba da aikin kula da bala'in ambaliyar ruwa da tsugunar da jama'a wadanda ibtila'in ya shafa.

Li Keqiang ya ce, yanzu ana cikin muhimmin lokaci na fama da bala'in ambaliyar ruwa a kasar, ba za'a yi kasala ba wajen daukar matakan da suka dace domin tunkarar bala'in da ake fama da shi a dai dai wannan lokaci.

Mista Li, ya kara da cewa, a lokacin da ake yin rigakafi da kuma fama da bala'in ambaliyar ruwa, dole ne a mai da hankali wajen kawar da haddura wadanda za su iya haddasa bala'in ambaliyar ruwa domin tabbatar da tsaron jama'a, da wasu muhimman ayyukan more rayuwa. Sannan, dole ne a mai da hankali wajen tsugunar da jama'a wadanda suke fama da bala'in domin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar. A cewarsa dole ne hukumomin da abin ya shafa su gaggauta kebe kudade da kayayyakin da ake bukata domin tabbatar da ganin jama'a sun samu kayan abinci da tufafi da tsabtaccen ruwa da aikin jinya da wuraren kwana na wucin gadi a kan lokaci. Bugu da kari, Li Keqiang ya ce, dole ne a dauki matakan tabbatar da ganin dalibai sun shiga makaranta a kan lokaci. Sannan, ya kamata a kara mai da hankali wajen yin rigakafin aukuwar annoba a wuraren da bala'in ambaliyar ruwan ta shafa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China