A ranar 15 ga wata, yayin da yake halartar taron karo na 31 na kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD, mukadashin jakadan zaunanniyar tawagar kasar Sin a ofishin Geneva na MDD mista Fu Cong, ya ce a wajen taron kasashen yammacin duniya su kan shafa wa kasashe masu tasowa kashin kaza wai suna keta hakkin dan Adam. Dangane da batun, a cewar Mr. Fu, idan har ana ci gaba da wannan yanayi a wajen kwamitin, to, mai yiwuwa ne kwamitin ya zama wata hukuma maras amfani. Don haka ya dace kasashen duniya su yi taka tsan-tsan don magance wannan sakamako.
Har ila yau mista Fu ya yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su daina nuna bambanci da raina sauran kasashe, su kuma yi zaman daidai wa daida, da nuna girmamawa kan yadda kasashen duniya suke raya hakkin dan Adam ta hanyoyi daban daban. Ya ce kamata ya yi a nuna adalci kan halin da wata kasa ke ciki ta fuskar kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, kana a yi kokarin daidaita sabani ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)